Nijar

Rahoton Ocha dangane da kisan fararen hula daga Boko Haram

Dakarun Najerya sun kwato wasu yankuna daga yan Boko Haram
Dakarun Najerya sun kwato wasu yankuna daga yan Boko Haram REUTERS/Emmanuel Braun

Majalisar dinkin Duniya ta ce ta damu ainun kan yadda a cikin wata guda mayakan Boko Haram sun kashe farraren hula 88 tare da tilasta wasu sama da dubu 18 barin gidajensu a yankin kudu maso gabashin kasar Nijar .

Talla

Ofishin dake kula da ayukan jinkai na Ocha dake birnin Yamai ya gano cewa hari 21 aka bayyana cewa, mayakan na boko haram suka kai kan farraren hula da jami'án tsaro a cikin watan maris din da ya gabata, inda sakamakon haka rayukan fararen hula 88 ne suka salwanta.

Hukumar ta bayyana cewa sakamakon wadannan hare hare dai ya tilastan kimanin mutane dubu 18.480 barin garuruwansu tareda kama hanya zuwa garin Diffa babban birnin jihar .

Ocha ta kara da cewa, yanzu haka yan gudun yakin na ci gaba da tururuwa zuwa garin na Diffa inda suke sauka a zanguna daban daban dake birnin.

Hukumar ta Ocha ta bayyana cewa lamuran tsaro sun gurbace a yankin na Diffa, dake gabar tafkin Chadi, kan iyakar kasashen Nijar,Najeriya,Kamaru.

Wadanan hare hare na mayakan kungiyar Boko Haram da ta samo asali daga Najeriya baya ga farraren hula sun yi sanadiyar salwantar rayukan sojojin kasar ta Nijar, a yayin da suka bankawa daruruwan gidajen jama’á wuta, tare da yin garkuwa da mata da dama a cewar hukumomin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI