Rwanda-Faransa

Bikin cikon shekaru 25 da kisan kiyashin Rwanda

Sunayen wasu daga cikin mutanen da suka rasa rayukan a kisan kiyashin Rwanda na shekara ta 1994
Sunayen wasu daga cikin mutanen da suka rasa rayukan a kisan kiyashin Rwanda na shekara ta 1994 AFP/Jacques NKinzingabo

yau ne jajuburin bikin tuni da kisan kiyashin kasar Rwanda da yayi sanadiyar mutuwar mutane akala dubu 800 a wannan kasa.Al’umar kasar Rwanda na bikin cika shekaru 25 da faruwar kisan kiyashin shekarar 1994 da ya yi sanadiyar salwantar da rayukan mutane ba tare da hukumta masu hannu a wannan kazamin aiki ba

Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ba zai halarci taruruka da addu’o’in cika sekaru 25 da barkewar kisan kiyashin kasar Rwanda da za a yi gobe ranar 7 ga watan afrilu.

Sakamakon kusancin da aka samu tsakanin Faransa da Rwanda bayan zuwan Macron karagar mulki, wannan ya sa gwamnatin Rwanda aike wa shugaban da goron gayyata domin ya halarci wadannan adu’o’I da za a yi a birnin Kigali, to sai dai Macron ya ce zai tura wani dan majalisar dokokin kasar mai suna Hervé Berville domin ya wakilce shi.

Hervé Berville maraya ne da ya tsira daga kisan kiyashin da aka yi 1994, kafin dauke shi zuwa Faransa lokacin yana da shekaru 4 a duniya.

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya share tsawon shekaru yana takun-saka da mahukuntan Faransa, bisa zargin cewa suna da hannu a wannan rikici da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 800 mafi yawansu ‘yan kabilar Tutsi marasa rinjaye a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI