Sabuwar zanga-zangar kungiyoyin farraren hula a Mali
A kasar Mali akala mutane dubu 30 ne suka fito a jiya a babban birnin kasar a wata zanga-zanga nuna adawa da rawar da hukumomin kasar ke takawa dangane da batutuwan da suka shafi rashin tsaro a yankunan kasar.
Wallafawa ranar:
Shugabanin adinai, kungiyoyin makiyaya, yan siyasa da kungiyoyin farraren hula ne suka shiga wannan zanga-zanga,tareda bukatar ganin Shugaban kasar Ibrahim Bubacar Keita ya salami wasu daga cikin ministocin sa da ake zargi da rashin nuna iyawa.Gwamnatin Mali ta nuna kaduwa bayan haukuwar kisan makiyaya a garin Ogossagou.
Ranar 23 ga watan Maris da ta gabata dai ne wasu mafarauta suka kashe makiyaya 160 a garin Ogossagou.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu