Najeriya-Zamfara

'Yan Najeriya na zanga-zanga kan kisan kiyashin da ake yi a Zamfara

Ko a jiya Juma'a 'yan Najeriya mazauna birnin London sun gudanar da makamanciyar zanga-zangar
Ko a jiya Juma'a 'yan Najeriya mazauna birnin London sun gudanar da makamanciyar zanga-zangar herald.ng

WASU Yan Najeriya yau sun gudanar da zanga zangar lumana a birnin Abuja da wasu biranen kasar domin nuna bacin ransu da irin matakan da gwamnatin kasar ke dauka na dakile kashe kashen da ake cigaba da yi a Jihar Zamfara wadanda suka gaza magance matsalar.

Talla

Rahotanni daga Abuja, sun ce masu zanga zangar akasarin su matasa da mata sun yi tattaki zuwa gaban ofishin shugaban kasa, duk da ya ke shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka na ziyarar aiki a kasar Jordan.

Daga Kaduna ma haka rahotan ya ke, inda masu zanga zangar suka bukaci sa ke dabarun murkushe 'yan bindigar da ke cigaba da kashe jama’a ba tare da kakkautawa ba.

Ko a jiya saida wasu Yan Najeriya mazauna birnin London suka gudanar da irin wannan zanga zangar bayan sun yi tattaki zuwa ofishin Jakadancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI