Sudan

'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Shalkwatar Sojin Sudan

Jami'an 'yansandan kwantar da tarzoma a zanga-zangar Sudan
Jami'an 'yansandan kwantar da tarzoma a zanga-zangar Sudan AFP

Jami'an kwantar da tarzoma a Sudan sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye kan dandazon masu zanga-zangar da suka taru a gab da shalkwatar rundunar sojin kasar yau Asabar.

Talla

Yau ne dai karon farko cikin fiye da watanni 3, da dubban masu zanga-zanga a Sudan suka samu damar isa ga Shalkwatar rundunar Sojin, inda su ke ihu tare da fadin soji 1 farar hula 1, duk dai a yunkurinsu na ganin shugaba Omar al-Bashir ya yi murabus.

Rahotanni sun ce ko bayan zuwan jami'an kwantar da tarzomar, masu zanga-zangar sun rika jifansu da duwatsu, suna cewa dole akawo karshen dokar tabaci da kuma mulkin Omar al-Bashir.

Tun bayan daukar matakin yiwa gwamnatinsa Garambawul da kuma sanya dokar ta baci a sassan kasar ranar 22 ga watan Fabrairu, tururuwar masu zanga-zangar ta karu tare neman lallai shugaban ya yi murabus bisa zarginsa da tsawwala rayuwa baya ga gurgunta tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI