Najeriya-Zamfara

Gwamnatin Najeriya ta Haramta hakar zinare a Zamfara

Jihar Zamfara mai arzikin zinare na cikin jihohin Najeriya da yanzu haka ke fama da matsalar tsaro
Jihar Zamfara mai arzikin zinare na cikin jihohin Najeriya da yanzu haka ke fama da matsalar tsaro Africa Finance Corporation

Gwamnatin Najeriya ta yi umarnin dakatar da hakar zinare a ilahirin sassan jihar Zamfara da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, a wani mataki na tabbatar da tsaro da kare asarar rayukan da ake fuskanta a jihar.

Talla

A jawaban babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, yayin wani taron manema labarai da ya kira yau lahadi, ya ce gwamnati ta dauki matakin ne bayan gano alaka tsakanin ‘yan bindigar da kuma masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

Daruruwan rayuka ne dai suka salwanta a sassan jihar ta Zamfara cikin shekarar nan sanadiyyar hare-haren ‘yan bindigar da ke kara ta’azzara.

Matakin dai na zuwa bayan wani gangami da ya gudana jiya a Abuja babban birnin Najeriyar da kuma wasu biranen kasar kan kisan kiyashin da ke ci gaba da gudana a jihar ta Zamfara mai arzikin zinare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI