Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun farmaki garin Kakangi a Kadunar Najeriya

Rahotanni sun ce cikin wadanda harin ya rutsa da su har da wadanda suka je biki garin na Kakangi
Rahotanni sun ce cikin wadanda harin ya rutsa da su har da wadanda suka je biki garin na Kakangi REUTERS/Afolabi Sotunde

Rahotanni daga Jihar Kaduna da ke Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun kai kazamin hari garin Kakangi da ke Birnin Gwari, inda suka harbe mutane da dama cikin su harda kananan yara.

Talla

Bayani sun ce da misalin karfe 5 na yammacin asabar, 'yan bindigan akan Babura suka bude wuta kan mai uwa da wabi kan jama’a da ofishin Yan Sanda, yayin da suka cinnawa gidajen jama’a wuta.

Rahotanni sun ce harin ya ritsa da mutane da dama masu halartar bikin aure, cikin su har da fitattun 'yan garin.

Jihar Kaduna dai na ci gaba da fama da matsalar hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane don karbar fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.