Sudan

Al'ummar Sudan na fatan samun canjin Shugabanci

Masu zanga-zanga a kasar Sudan
Masu zanga-zanga a kasar Sudan AFP/A. Shazly

Ministan Harkokin cikin gida na kasar Sudan Bushara Juma ya sanar da cewa mamata sakamakon zanga-zangan kasar sun kai 6 ya zuwa yau Littini.Ministan ya ce akwai mutane 15 da wasu jamian tsaro 42 da suka jikkata.

Talla

Ga duk alamu, wasu daga cikin sojojin sun nuna alamar bai wa masu zanga-zangar kariya bayan wasu jami’an tsaro na daban sun harba hayaki mai sa kwalla kan masu zanga-zangar da suka yi zaman dirshen,

Shaidu sun ce, sojojin sun yi fatattaki wasu manyan motoci da ke cilla barkonon-tsohuwa kan masu zanaga-zagar.

Masu zanga-zangar na fatan sojojin za su yi wa shugaban kasar juyin mulki bayan ya shafe kusan shekaru 30 a kan karagar mulki.

Kawo yanzu, shugaba al-Bashir ya ki amincewa da bukatar kafa gwamnatin rikon kwarya duk da tsawon lokacin da aka shafe na gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.