Libya

Haftar na kan hanyar karbe Tripoli

Dakarun Janar Haftar a harabar babban birnin Tripoli
Dakarun Janar Haftar a harabar babban birnin Tripoli REUTERS/Esam Omran Al-Fetori

Karfa karfar janar din sojin da ke rike da yankin gabashin kasar Libya Khalifa Haftar, na ci gaba da nausawa zuwa birnin Tripoli a yau litanin,yayinda rahotanni daga yankin ke nuna cewa mutane 35 ne suka mutu a gumurzu da ya hada dakarun Haftar da sojan Al Sarraj.

Talla

A sabon fadan da ya kaddamar da nufin kwace birnin Tripoli babban birnin kasar Libiya, inda aka bayyana cewa ana ci gaba da gwabza fada a unguwanin dake bakin kofar shiga birnin,akalla mutane 35 ne suka mutu yayinda wasu 80 suka samu raunuka.

To domin jin hali da kuma zullumin da al’úmma ke ciki a birnin, Alhasan Maidaji, wani dan Nijar mazauni Tripoli, ya yi mana tsokaci a kai

Dakarun Janar Haftar kan hanyar kama Tripoli

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.