Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta kai hari Damaturu karon farko bayan 2014

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai farmaki garin Damaturu na jihar Yobe karon farko bayan harin shekarar 2014, matakin da ya tilastawa dubban jama’a tserewa don gujewa fadawa karkashin mulkin kungiyar.

Wasu dakarun sojin Najeriya
Wasu dakarun sojin Najeriya AFP Photo/ISSOUF SANOGO
Talla

Wani ganau ya shaidawa manema labarai cewa, mayakan sun rika harbi tare da jefa bama bamai a sassan jihar.

Rahotanni sun ce bayan shigar mayakan garin na Damaturu da misalin karfe 5 :45 na yammaci anga manyan motocin soji na shiga garin don fafatawa da su.

Hashimu Idris, wani ma’aikacin gwamnati ya ce sun shiga gidajensu sun kukkule tare da addu’ar Sojojin su yi nasarar fatattakar mayakan na Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI