Najeriya-Dubai

'Yan Najeriya 446 na daure a gidajen yarin Dubai- Gwamnati

Ko cikin watan jiya sai da aka kame wasu tarin 'yan Najeriya a Saudiya saboda aikata ba dai dai ba
Ko cikin watan jiya sai da aka kame wasu tarin 'yan Najeriya a Saudiya saboda aikata ba dai dai ba google.com

Gwamnatin Najeriya ta ce yanzu haka 'yan kasar 446 na tsare a gidajen yarin kasar Hadaddiyar Daular Larabwa saboda aikata laifuffukan da ke da nasaba da safarar kwayoyi da kuma wasu laifuffuka.

Talla

A jawaban da ya gabatar gaban taron 'yan Najeriya mazauna kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin wata ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari a ziyarar da yanzu haka ya ke ci gaba da yi a kasar, Jakadan Najeriyar a birnin Dubai, Ambasada Mohammed Dansanta Rimi akwai tarin 'yan Najeriya da ke aikata ayyukan assha a kasar.

Kalaman na Ambasada Mohammed Dansamta Rimi na zuwa ne makwanni kalilan bayan kame wasu 'yan Najeriyar guda 5 da ake zargi da laifin fashi da makami a Kasar.

Ka zalika ko cikin watan jiya an yanke wasu tarin 'yan Najeriya hukuncin kisa wasu kuma daure a gidajen yarin Saudiya bayan samunsu da aikata ba dai dai ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.