Afrika ta Kudu-Libya

Babu kudin Ghadafi a hannuna- Zuma

Tsohon Shugaban Kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya ki amincewa da zargin da ake masa cewar yana rike da kudaden tsohon shugaban kasar Libya Mu'ammar Ghadafi da suka kai Dala miliyan 30.

Marigayi Mu'ammar Ghadafi
Marigayi Mu'ammar Ghadafi REUTERS/Huseyin Dogan
Talla

Jaridar Sunday Times a karshen mako ta ruwaito cewar, jim kadan kafin hallaka Ghadafi a shekarar 2011, ya aika wa shugaba Zuma da kudin domin adana masa.

Jaridar ta ce, shugaba Zuma ya ajiye kudaden a kauyensu da ke Nkandla kafin daga bisani ya mayar da su kasar eSwatini da a wancan lokacin ke amsa sunan kasar  Swaziland.

Gidauniyar Zuma ta bayyana labarin a matsayin na kanzon-kurege, wanda ba shi da tushe ballanatana makama, in da ta ce, Zuma ba shi da masaniya akai.

Shi ma tsohon shugaban ta kafar Twitter ya yi watsi da zargin, in da yake cewa shi da ya kasa biyan lauyoyin da ke kare shi a kotu, ina zai samu wadannan makudan kudade.

Ministan Harkokin Wajen Afrika ta Kudu Lindiwe Sisulu shi ma ya ce, babu gaskiya cikin labarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI