sudan

Sojin Sudan na goyon bayan masu zanga-zanga

Masu zanga-zanga a harabar shalkwatan rundunar sojin Sudan
Masu zanga-zanga a harabar shalkwatan rundunar sojin Sudan AFP/A. Shazly

Jami’an Sojin Sudan na nuna alamar goyon bayansu ga masu zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar, abinda ke nufin cewa, sun fara dawowa daga rakiyar shugaba Omar al-Bashir da ya kwashe shekaru 30 bisa madafun iko.

Talla

Dubun dubatan masu zanga-zangar na ci gaba da zaman-dirshen a harabar shalkwatan rundunar sojin Sudan da ke dauke da gidan gwamnati, in da shugaba al-Bashir ke zaune.

Rahotanni sun ce, masu zanga-zangar sun yi ta daukar jami’an sojoji akan kafadunsu tare da rera wake-wake da raye-raye da sojojin.

Kazalika masu boren sun yi ta mika gaisuwar ban-girma ga sojojin cikin farin ciki, lamarin da masharhanta irinsu Magdi El Gizouli na cibiyar Rift Valley, suka fassara da wata alama da ke nuna cewa, sojojin na goyon bayan masu zanga-zangar a Sudan.

Masharhantan sun ce, zanga-zangar ta sauya matsayar sojojin kasar da a can baya suka yi tsayin-daka wajen tabbatar da mulkin al-Bashir na tsawon shekaru 30.

Tun da farko, masu zanga-zangar sun bukaci sojojin da su goyi bayansu kan yunkurinsu na kawar da gwamnatin shugaba al-Bashir.

Ko a ranar Litinin da ta gabata, sai da kungiyoin kare hakkin bil’adama suka bukaci rundunar sojin kasar da ta gudanar da tattaunawar kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar.

Ita ma rundunar ‘yan sandan kasar ta garagadi jami’anta da su kauce wa tsoma baki kan zanga-zangar, tana mai fatan za a samar da hanyar lumana wajen kafa gwamnatin rikon kwaryar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.