Sudan

Sojoji sun hambarar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir na Sudan

Rahotanni daga kasar Sudan na cewa sojoji sun kwace iko tare da kame shugaba Omar Hassan al-Bashir da ilahirin mukarraban gwamnatinsa, a safiyar yau Alhamis bayan tsanantar zanga-zangar kin jinin gwamnati a sassan kasar.

Wasu al'ummar Sudan da ke dakon jawabin rundunar Soji
Wasu al'ummar Sudan da ke dakon jawabin rundunar Soji Photo: AFP
Talla

Cikin jawaban da sojin suka gabatar a yau, sojin sun ce za su ci gaba da jan ragamar gwamnatin rikon kwarya har zuwa nan da shekaru 2.

Rahotanni sun ce an rufe tashar jiragen saman Khartoum, yayin da shaidun gani da ido suka ce sun ga motocin soji da dama dauke da dakaru ana girke su a sassan birnin.

Tashar Aljazeera ta nuna masu zanga zangar dauke da tutar Sudan na murna, suna cewa, ya fadi, mun kuma samu nasara, yayin da gidajen talabijin da rediyo na kasar ke sanya kade kaden da ke kara kaimin 'yan kasa da aka saba sanya su lokacin juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI