Najeriya-wasanni

Golden Eaglets ta isa Tanzania don fafatawa a gasar cin kofin Afrika

Tawagar 'yan wasan Najeriya ta 'yan kasa da shekaru 17 Golden Eaglets a Tanzania
Tawagar 'yan wasan Najeriya ta 'yan kasa da shekaru 17 Golden Eaglets a Tanzania News Agency of Nigeria (NAN)

Tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya ta ‘yan kasa da shekaru 17 Golden Eaglets ta bar Abuja zuwa Tanzania don taka leda a gasar cin kofin Nahiyar Afrika ta ‘yan kasa da shekaru 17 karo na 13 da za ta fara gudana ranar 14 zuwa 28 ga watan nan.

Talla

Golden Eaglets wadda ta dage kofin duniya har sau biyar, ta samu tikitin zuwa Tanzaniyar ne bayan nasara a gasar WAFU ta kasashen yammacin Afrika cikin watan Satumban bara a Jamhuriyar Nijar, bayan da ta lallasa Ghana da kwallaye 3 da 1 a wasan karshe.

Yanzu haka dai tawagar ta Golden Eaglets wadda ta halarci makamanciyar gasar har sau 9 ta kuma lashe sau 2 a shekarar 2001 da 2007 na cikin kasashen Afrika 4 da za a ga tutarsu a gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 da Brazil za ta karbi bakonci.

Yayin gasar ta tsawon mako guda a Tanzania dai, Golden Eaglets wadda ke rukunin A za ta kara da mai masaukin baki Tanzania kana Uganda sai kuma Angola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI