Faransa-Ta'addanci

Sojin Faransa sun hallaka 'yan ta'adda 30 akan iyakar Mali da Burkina Faso

Sojin Faransa a Mali
Sojin Faransa a Mali REUTERS/Eric Gaillard

Rundunar sojin Faransa ta ce dakarunta da hadin gwiwar na kasar Mali sun yi nasarar hallaka mayakan jihadi fiye da 30 yayin wani gumurzu tsakaninsu cikin makon jiya a gab da kan iyakar Mali da Burkina Faso.

Talla

Sanarwar rundunar sojin ta Faransa ta ce tun a ranar 2 ga watan nan ne dakarun na ta suka kaddamar da farmakin kan 'yan ta'addan masu ikirarin jihadi, harin da ya haifar da gagarumar koma baya a tsare-tsaren 'yan ta'addan.

Yayin Farmakin na makon jiya, wani likitan sojin na Faransa ya rasa ransa sanadiyar taka nakiya da motarsu ta yi a yankin Gurma da ke tsakiyar gabashin Mali.

A jimilce da dakarun rundunar sojan Faransa Barkhane 700 da sojan Mali 150 ne aka tanada a aikin, da ya fara daga sansanin sojan Mali da ke Hombori mai tazarar kilomita 80 arewacin kan iyakar kasar da Burkina Faso.

Kakakin sojin Faransa Kanal Patrik Steiger, ya ce a bangaren Burkina Faso an saka sojan kasar cikin shiri domin hana kutsen 'yan ta'addan daga kudanci kasar,

Bayan share tsawon shekara daya da rabi na fada da masu ikararin Jihadi a yankin Liptako, dake hannun riga da yankunan (nord-est) mali, runduna sojan Barkhane ta kara matsa kaimi wajen fadada ayukanta a wannan sabon yanki, da ke makwabtaka da yankunan kasar Mali uku (Gao, Tombouctou da kuma Mopti) da suka hada iyaka da Burkina Faso.

A baya bayan nan, sojan Faransa suka sake kafa wani sansani a wajen garin Gossi mai tazarar kilo mita 150 yammacin Gao da ke arwacin Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.