Sudan

Sojoji za su yi mulkin shekaru biyu a Sudan

Ministan Tsaron Sudan  Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf a yayin gabatar da jawabi ta kafar talabijin
Ministan Tsaron Sudan Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf a yayin gabatar da jawabi ta kafar talabijin Sudan TV/ReutersTV via REUTERS

Sojojin Sudan da suka kifar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir, za su ja ragamar kasar na tsawon shekaru biyu kafin gudanar da sabon zaben shugaban kasa.

Talla

Ministan Tsaron Kasar, Awad Mohammed Ahmed Ibn Ouf ya bayyana haka a yayin gabatar da jawabi ga al’ummar kasar ta kafar talabijin a ranar Alhamis jim kadan da cafke shugaba al-Bashir.

Ministan ya kuma kara da cewa, sun kafa dokar ta-baci ta tsawon watanni uku, yayinda ya ce, kasar ta tsunduma cikin matsaloli da dama da suka hada da cin hanci da rashawa da rashin adalci har ma da rashin jagoranci na gari.

Ministan ya bayar da hakuri kan asarar rayukan da aka samu da kuma tashe-tashen hankulan da suka barke a yayin gudanar da zanga-zangar kin-jinin shugaba al-Bashir.

Tuni aka dakatar da aiki da kundin tsarin mulkin kasar, yayinda aka rufe kan iyakokin kasar har sai baba-ta-gani, baya ga dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na tsawon sa’o’i 24.

Kawar da gwamnatin al-Bashir da ya shafe shekaru 30 akan karagar mulki na zuwa ne bayan zanga-zangar adawa da gwamnatinsa da al’ummar kasar suka gudanar.

Kodayake jagororin da suka shirya zanga-zangar sun bukaci a ci gaba da gudanar da ita duk kuwa da cewa, sojoji sun karbe iko da tafiyar da gwamnatin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.