Sudan

Ba za mu mika al-Bashir ga kotun duniya ba- Sojoji

Shugaban Kwamitin Majalisar Kolin Sojin Sudan, Omar Zain al-Abdin.
Shugaban Kwamitin Majalisar Kolin Sojin Sudan, Omar Zain al-Abdin. AFP/ A. Shazly

Kwana daya bayan ta karbe mulki, Majalisar Kolin Sojin Sudan ta ce, ba za ta mika hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir da ke fuskantar tuhume-tuhumen da suka shafi kisan kiyashi da laifukan yaki ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ba.

Talla

A jawabin da ya yi wa taron manema labarai, shugaban kwamitin siyasa na gwamnatin sojin Sudan, Laftanar Janar Omar Zain al-Abdin ya ce, a halin yanzu,  hambararren shugaban yana hannunsu, yana mai cewa, a matsayinsu na sojoji masu tafiyar da al’amura a kasar, ba za su mika shi ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ba.

Sau biyu kotun hukunta manyan laifuka ke aike wa da takardar neman a mika mata tsohon shugaba Omar al-Bashir, sakamakon laifukan yaki da keta hakkin bil'adama da ta ce ya aikata a yankin Dafur a tsakanin shekarun 2003 da 2008.

A halin da ake ciki, Majalisar Kolin Sojin ta shaida wa al’ummar kasar cewa, babban abinda yake gabanta, shi ne tabbatar da doka da kuma tafiyar da al’amuran kasa a tsanake.

A Juma’ar nan, jagoran Majalisar Soji, wadda shi ne Ministan Tsaro a gwamnatin al-Bashir, Awad Ibn Ouf, ya yi kashedin cewa, ko kadan ba za su lamunci birkita tsaro a kasar ba, bayan masu zanga-zanga sun yi kunnen-kashi da dokar takaita fitar dare don ci gaba da zaman-dirshen na neman a dawo da mulkin farar hula ba tare da bata lokaci ba.

A ranar Alhamis ne sojoji suka hambarar da shugaban Sudan, bayan masu zanga- zanga sun shafe watanni da dama suna gangamin kin jinin gwamnati, wanda ya samo asali daga karin farashin burodi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.