Sudan

Jagoran juyin mulkin Sudan ya yi murabus

Janar Ibn Auf a lokacin da ya sanar da sauka daga mukamin Shugaban sojan kasar Sudan
Janar Ibn Auf a lokacin da ya sanar da sauka daga mukamin Shugaban sojan kasar Sudan Sudan TV / AFP

Wasu sojoji a Sudan sun yi kokarin kifar da Majalisar kolin sojin kasar da ta sauke al Bashir mai shekaru 75 daga madafun ikon kasar yau.Kwanaki 3 bayan kifar da gwamnatin ta Sudan da soji suka yi, ministan tsaron kasar Awad Ibn Ouf da ke rike da madafan iko bayan ficewar Al Bashir ya sanar da sauka bayan tsanantar zanga-zanga a Khartoum.

Talla

Tsohon Ministan tsaron kasar dake rike da madafan ikon kasar ta Sudan ya mika ragama zuwa daya daga cikin manyan hafsan sojan kasar mai suna Abdel Fattah Al Burhan Abdelrahmane.

Idan aka yi tuni Majalisar Sojin kasar ta Sudan bayan kifar da Al Bashir ta ce ba za ta mika hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir da ke fuskantar tuhume-tuhumen da suka shafi kisan kiyashi da laifukan yaki ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ba.

A jawabin da ya yi wa taron manema labarai, shugaban kwamitin siyasa na gwamnatin sojin Sudan, Laftanar Janar Omar Zain al-Abdin ya ce, a halin yanzu, hambararren shugaban yana hannunsu, yana mai cewa, a matsayinsu na sojoji masu tafiyar da al’amura a kasar, ba za su mika shi ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ba.

Sau biyu kotun hukunta manyan laifuka ke aike wa da takardar neman a mika mata tsohon shugaba Omar al-Bashir, sakamakon laifukan yaki da keta hakkin bil'adama da ta ce ya aikata a yankin Dafur a tsakanin shekarun 2003 da 2008.

A jiya Juma’ar nan, jagoran Majalisar Soji, wadda shi ne Ministan Tsaro a gwamnatin al-Bashir, Awad Ibn Ouf, ya sanar da sauka daga mukamin nasa ,bayan haka ya yi kashedin cewa, ko kadan ba za su lamunci birkita tsaro a kasar ba, bayan masu zanga-zanga sun yi kunnen-kashi da dokar takaita fitar dare don ci gaba da zaman-dirshen na neman a dawo da mulkin farar hula ba tare da bata lokaci ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI