Sudan

Shugaban sashen fikira na Sudan ya yi murabus

Laftanal Janar Omar Zain al-Abdin (C), saboon shugaban harkokin siyasa na rikon kwarya a Sudan
Laftanal Janar Omar Zain al-Abdin (C), saboon shugaban harkokin siyasa na rikon kwarya a Sudan ASHRAF SHAZLY / AFP

Shugaban sashen fikira na Sudan ya sanar da ajje mukaminsa yau asabar kwana guda bayan shugaban rikon kwaryar da ya maye gurbin shugaba Omar al-Bashir ya yi murabus sakamakon ci gaban zanga-zanga a kasar ta neman mulkin farar hula ba soji ba.

Talla

Salah Abdallah Mohammed Saleh, wanda aka fi sani da Salah Gosh, shi ne mutum na biyu mai karfin fada aji a kasar bayan Omar al-Bashir, kuma shi ne ake zargi da umarnin duk kisan da jami’an tsaro suka yi lokacin zanga-zangar kasar ta fiye da watanni 4.

Tuni dai shugaban hukumar tsaro na kasar ta Sudan Laftanal Janar Abdel Fattah al-Burhan ya karbi murabus din Salah Gosh.

Yanzu haka dai al'ummar Sudan na ci gaba da bore kan lallai a samar musu da gwamnatin farar hula sabanin mulkin soji da sashen tsaron kasar ke kokarin yi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.