Libya-Masar

Al-Sisi ya gana da Haftar na Libya kan sabon rikicin Tripoli

Babban kwamandan askarawan da ke mamaye da yankin gabashin Libya Khalifa Haftar a ganawarsa da Abdel Fattah al-Sisi na Masar a birnin alkahira
Babban kwamandan askarawan da ke mamaye da yankin gabashin Libya Khalifa Haftar a ganawarsa da Abdel Fattah al-Sisi na Masar a birnin alkahira Reuters

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya gana da Khalifa Haftar na Libya a birnin alkahira, dai dai lokacin da Haftar ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan hare-haren da ya ke kaiwa Tripoli da nufin kwace birnin.

Talla

Shugaba al-Sisi dai na matsayin aminin Khalifa Haftar, wanda ke rike da ikon gabashin kasar kafin karbe ragama da kudanci gabanin fara yunkurin kwace iko da Tripoli a kwanaki 10 da suka gabata.

Mai magana da yawun shugaba al-Sisi ya ce shugaban ya gana da Haftar ne game da halin da ake ciki yanzu haka a Libya, dai dai lokacin da Majalisar dinkin Duniya ke cewa rikicin ya hallaka mutane 120 tare da jikkata 600.

Kawo yanzu dai babu cikakkun bayanai daga bangarorin biyu yadda tattaunawar ta gudana ko kuma matakan da za a dauka dai dai lokacin da rikicin na Libya ke kara tsananta, sai dai fadar gwamnatin Masar ta fitar da wani hoto da ke nuna al-Sisi tare da Haftar a gefe kuma ga shugaban sashen Fikira na Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI