Afrika

Taron kawo karshen rikicin Sudan A Chadi

Shugabanin kasashen kungiyar yankin Sahara da aka sani da CEN SAD sun gudanar da wani taron gaggawa a Chadi a jiya asabar.Taron da ya mayar da hankali zuwa ga rikicin kasar Sudan .

Janar Abdel Fattah Abdelrahman sabon Shugaban majalisar sojin Sudan
Janar Abdel Fattah Abdelrahman sabon Shugaban majalisar sojin Sudan Sudan TV / AFP
Talla

Shugaban Chadi Idris Deby Itno ya bayyana damuwa matuka da cewa yanayin da wasu kasashe ke dab da fadawa kan iya haifar da wani sabon rikici a kan iyakokin kasashen su, yayinda shugaban hukumar zartarwa ta kungiyar Afrika Moussa Faki Mahamat, kasashen Afrika na cikin wani mauyacin hali,Afrika ta kasance wani yanki da yanzu tsaro da kwantiar hankali suka kaura.

A kasar ta Sudan jam’iyyar tsohon Shugaban kasar Omar El Beshir ,jam’iyyar NCP ta kalubalanci juyin mulki da sojojin kasar suka yi, ta kuma bukaci ganin an sako ilahirin shugabanin ta dake tsare yanzu haka.

A karshe jam’iyyar a wata sanarwa da ta fitar na nuni cewa kwace mulki ta hanyar kifar da gwamnati ya sabawa kudin tsarin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI