Chad

Sojojin Chadi sun kashe 'yan Boko Haram 63

Wasu daga cikin dakarun sojin Chadi da ke yaki da Boko Haram
Wasu daga cikin dakarun sojin Chadi da ke yaki da Boko Haram Reuters/路透社

Akalla mayakan Boko Haram 63 sun rasa rayukansu a wani dauki-ba-dadi da sojojin Chadi a cikin daren da ya gabata.

Talla

Mai magana da yawun sojin kasar, Kanar Azeem Bermandoa ya ce, an kashe musu jami’ai bakwai tare da jikkata 15 a harin da mayakan na Bokio Haram suka kaddamar kan sansanin sojin da ke Bouhama a yankin Tafkin Chadi.

Bermandoa ya kara da cewa, a halin yanzu suna kan farautar sauran mayakan na Boko Haram bayan sun kashe 63 daga cikinsu.

Ko a  watan jiya, sai da Boko Haram ta kashe sojoji 23 a Yankin Tafkin Chadi, harin da ake kallon sa a matsayin mafi muni da kungiyar ta kai kan dakarun sojin Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI