Afrika

Kamata Afrika ta Kudu ta gurfanar da wadanda suka haddasa rikicin kyamar baki

Rikici da baki yan kasashen waje a Afrika ta kudu
Rikici da baki yan kasashen waje a Afrika ta kudu ibtimes.co.uk

Kungiyar kare hakkin bil’ Adama ta Human Rights Watch ta bukaci hukumomin Afrika ta Kudu da su gurfanar da wadanda suka haddasa rikicin tsananin kyamar baki da ya yi sanadiyar hallaka da bacewar wasu ‘yan gudun hijirar Malawi kimanin 300 makonni uku da suka gabata.

Talla

Kungiyar HRW, daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Maris, wasu 'yan Afrika ta Kudu masu tsananin kyamar baki dauke da karafu da adduna suka farma gidajen baki ‘yan kasashen waje dake zaune a yankin Durban na gabar ruwar Gabashin kasar, inda suka tarwatsa su tare da awon gaba da kaddarorin su.

Babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce, akalla baki ‘yan kasashen waje shida sun mutu, wasu da dama sun jikkata sakamakon farmakin, lamarin da ke kara fargabar yawaitar tashin hankali mai zubar da jini sanadiyar kyamar baki a kasar ta Afirka ta Kudu, inda matalautar ‘yan kasar masu zaman kanshe wando ke zargin baki masu hazaka da mamaye musu sana’o’insu.

Kimanin mutane 88 da suka tsira daga harin na Durban sun bukaci a mayar da su zuwa kasarsu Malawi, kamar yadda ofishin jakadancin Malawi a kasar ya sanar, yayin da wasu da suka ce basu da wani zabi suka bukaci zama cikin yanayi da bashi da tabbas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.