EFCC ta cafke mai shari'a Rita bayan kammala yi mata shari'ar rashawa
Wallafawa ranar:
Jami'an hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, sun sake cafke tsohuwar mai shari Rita Ofili-Ajumogobia yau a kotun Lagos, jim kadan bayan alkalin da ke mata shari’a ya soke tuhumar da ake mata kan cin hanci da rashawa.
Rahotanni sun ce akalla jami’an EFCC guda goma suka yi wa tsohuwar mai shari’ar kawanya lokacin da ta fito daga kotun ta na neman tafiya gida.
Wasu bayanai na nuni da cewa kokarin tsohuwar mai shari'ar na rugawa cikin kotun don samun kariya ya ci tura, haka zalika yayin da aka shaidawa alkalin kotun Hakeem Oshodi halin da tsohuwa mai shari’ar ke ciki, sai ya ce tuni ya kammala wancan shari’ar da ake mata.
Mai shari’a Rita Ofili-Ajugomobia na daya daga cikin manyan alkalan Najeriya da hukumar DSS ta kama saboda zargin cin hanci da rashawa, abinda ya tilasta mata barin aiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu