Kenya

An sace makaman 'yan sanda da ke kallon wasan kwallo

Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Kenya
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Kenya REUTERS/Thomas Mukoya

Wasu gaggan barayi sun fasa ofishin ‘yan sandan Kenya, in da suka sace makamai a daidai lokacin da jami’an ‘yan sandan ke kallon wasan Barcelona da Manchester United a gasar zakarun Turai a ranar Talata a wani gidan kallo.

Talla

Jaridun Kenya sun rawaito cewa, barayin sun sace manyan bindigogi uku da kuma jigidar alburusai na ‘yan sandan Kobujoi da ke lardin Nandi a kasar.

Bayan ‘yan sandan sun dawo daga gidan kallon ne suka tarar an fasa dakin ajiyar makamansu.

Rahotanni na cewa, ana ci gaba da bincike da kuma farautar barayin da suka sace makaman.

Tuni wannan al’amari ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta a kasar, in da wasu ke zargin ‘yan sandan da yin sakaci da aikinsu na kare lafiya da dukiyar al’umma duk da kudin albashi da ake biyan su domin wannan aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.