Najeriya-Atiku-Buhari

Zan gayyato kwararru daga Amurka don tabbatar da nasarata- Atiku

Dan takarar shugabancin Najeriya na Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar
Dan takarar shugabancin Najeriya na Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar REUTERS/Nyancho NwaNri

Dan takarar shugabancin Najeriya na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce ya na gab da gayyato kwararru daga Kamfanonin fasaha na Microsoft da IBM da kuma Oracle don tabbatar da zarginsa na cewa shi ne ya lashe zaben kasar na watan Maris.

Talla

Atiku Abubakar dai ya yi ikirarin cewa hatta shafin hukumar zaben Najeriyar mai zaman kanta INEC ya tabbatar da cewa ya doke Muhammadu Buhari na APC da kuri’un da yawansu ya kai miliyan 1 da dubu dari 6.

Kalaman na Atiku na zuwa ne bayan martinin INEC kan ikirarin sa cikin makon jiya na cewa ya gano shi ke da nasarar, inda hukumar ta INEC ta ce ba daga shafinta ya samu bayanansa ba.

Sai dai Atiku Abubakar ya ce sakamakon wanda aka yiwa suna da INEC_PRES_RSLT_SRV2019 na kunshe a wani kundi mai adireshi kamar haka 94-57-A5-DC-64-B9 da lamba tantancewa ta ID 00252-70000-0000-AA535.

A cewar Atiku Abubakar sakamakon da ke kunshe cikin Kundin ya nuna ya samu kuri’u 18,356,732 wanda ya kayar da shugaba Muhammadu Buhari na APC wanda ya samu kuri’u 16,741,430.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.