Sudan

Gwamnatin Sudan ta kame shakikan al-bashir 2 bayan jefa shi a Yari

Hoton matan da ke ci gaba da zanga-zanga a Sudan
Hoton matan da ke ci gaba da zanga-zanga a Sudan 路透社

Gwamnatin rikon kwarya ta mulkin Soji a Sudan ta kame biyu daga cikin shakikan hambararen shugaban kasar Omar al-Bashir bayan daukar matakin jefa shi a gidan yarin kasar, duk dai karkashin matakan gyara da ta ke dauka bayan nasarar yin juyin mulki a makon jiya. 

Talla

A jawaban da ya gabatar gaban manema labarai cikin yammacin jiya a birnin Khartoum, mai rike da mukamin kakakin gwamnatin Sojin Laftanal Janar Shamsudden Kabbashi ya ce sun kame biyu daga cikin shakikan Omar al-Bashir biyar, wadanda ya ce suma za su ci gaba da zama a yari tare da shi.

Tuni dai gwamnatin Sojin ta aike da al-Bashir gidan yarin Kober da ke birnin na Khartoum bayan tsanantar masu zanga-zanga wadanda suka yi zaman dirshan a harabar fadar gwamnatin.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International dai na ci gaba da gargadin gwamnatin sojin ta rukon kwarya kan ta gaggauta mika al Bashir gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC don amsa tuhumar da ake masa ta aiwatar da kisan kare dangi baya ga taimakawa wasu kungiyoyin ta'adda.

Ko a yau Alhamis ma dai zanga-zanga a sassan kasar ta Sudan ta ci gaba da gudana ciki har da mata zalla wadanda ta kunshi jami'an lafiya 'yan jarida da kuma jami'an tsaro.

Har yanzu dai al'ummar Sudan na neman lallai Sojin su mika al Bashir gaban kotu don fuskantar hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI