Najeriya-Boko Haram

Sojin hadaka sun hallaka mayakan Boko Haram 52 a gabashin Najeriya

Wasu dakarun sojin Chadi a Gamborou
Wasu dakarun sojin Chadi a Gamborou REUTERS/Emmanuel Braun

Rundunar sojin Najeriya ta ce Dakarun hadaka sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram fiye 50, a wani farmaki da suka kai maboyarsu a yankin arewa maso gabashin kasar ranar Talatar da ta gabata.

Talla

Cikin sanarwar da Kanal Azem Bermandoa ya fitar a jiya, ta ce sumamen dakarun sojin ya hallaka mayakan na Boko Hram 52 tare da samun nasarar kwace wasu tarin makamai da ababen hawa.

Sai dai yayin farmakin a cewar Kanal Bermandoa, sojin Jamhuriyar Chadi 2 sun rasa rayukansu, baya ga wasu soji 11 da suka samu raunuka.

Dakarun wanda na hadaka ne sun kunshi na Chadi Kamaru, Nijar da kuma Najeriya, dukkaninsu kasashen da ke fuskantar barazanar hare-haren Boko Haram cikin kusan shekaru 10 da suka gabata.

Cikin watan Fabarairun da ya gabata ne dai dakarun kasar Chadi fiye da 500 suka shiga Najeriya don taimakawa a yaki da Boko Haram, inda ko a Lahadin da ta gabata ma sai da 7 suka rasa rayukansu a wani harin Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI