Najeriya

Buhari ya kara wa'adin mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya

Mukaddashin alkalin alkalan Najeriya, mai shari'a Tanko Muhammad
Mukaddashin alkalin alkalan Najeriya, mai shari'a Tanko Muhammad NAN

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara wa’adin aikin Babban mai shari’ar kasar na riko, Tanko Muhammad zuwa nan da watanni uku.

Talla

Daraktan yada labaran hukumar da ke kula da ayyukan shari’a a Najeriya, Soji Oyi ya ce shugaba Buhari ya gabatar da bukatar karin wa’adin ga hukumar wadda a zaman da ta yi ranar alhamis ta amince da hakan.

A watan Janairun da ya gabata ne shugaba Buhari ya nada Mai shari’a Tanko Muhammad a matsayin Babban mai shari’a na riko bayan dakatar da mai rike da kujerar Walter Onnoghen wanda aka tuhuma da laifin kaucewa bayyana kadarorin sa da kuma boye asusun ajiyar kudaden kasashen waje.

Tuni kotun ladabtar da ma’aikata ta samu Onnoghen da laifi, inda ta haramta masa rike duk wani mukami na shekaru 10 da kuma mallakawa gwamnatin Najeriya asusun da ke dauke da kudaden ajiyar sa guda 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.