Afrika

Sabuwar zanga-zanga a Tripoli

Janar Haftar a fadar sa dake birnin Bhengazi na kasar Libya
Janar Haftar a fadar sa dake birnin Bhengazi na kasar Libya REUTERS/Esam Omran Al-Fetori

A babban birni Tripoli na kasar Libya dubban jama’a ne sanye da riguna kalar dorowa suka gudanar da zanga-zanga nuna adawa da janar Haftar da yanzu haka dakarun sa suka kaddamar da yaki na karbe ikon Tripoli.Masu zanga-zangar sun kuma la’anci Faransa da suke zargi da goyawa Janar Haftar baya.

Talla

A dai-dai lokacin da wannan zanga-zanga ta kuno kai a Libya ,Amurka ta fito fili tareda bayyana goyan bayan ta zuwa Janar Haftar,rahotanni sun nuna cewa Janar Haftar ya tattauna ta wayar talho da Shugaban Amurka Donald Trump.

Wasu kasashen Duniya na sukar matakin Amurka bayan da al’umar Tripoli suka bayyana adawa da matakan soja daga Janar Haftar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.