Afrika

An fara zaben tsawaita wa'adin Shugaba al Sisi na Masar

A yau asabar al’ummar kasar Masar na kada kuri’a raba gardama a zaben da zai bai wa Shugaban kasar Abdel Fattah Al- Sisi damar kawo gyara ga kudin tsarin mulkin kasar don ci gaba da zama a kujerar mulkin kasar har zuwa shekara ta 2030.

Masu zabe a kasar Masar
Masu zabe a kasar Masar REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Mutane milyan 62 ne hukumar zaban kasar ta tattance da kuma za su bayyana zabin su tsawon kwanaki uku dangane da kawo gyara ga kudin tsarin mulkin kasar Masar, wata hanyar sake baiwa shugaban kasar mai ci Abdel Fattah-al Sissi cikakken mulki da kuma sake tsayawa takara a zaben shekarar 2024 zuwa shekara ta 2030.

Akasarin yan kasar sun yaba da wannan bukata daga Shugaban kasar ,lalurar su itace Shugaban kasar ya ci gaba da tabbatar da tsaro da kuma samarwa jama’a kayakin more rayuwa kamar dai yada aka saba gani a wannan tafiya da Shugaban kasar Abdel Fattah-al Sissi.

A shekara ta 2014 ne aka zabe Abdel Fattah-al Sissi da kusan kashi 96 cikin dari na kuri’u da aka kada,shekara daya bayan juyin mulki da sojojin kasar suka yiwa Mohamed Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI