Motar soji ta taka nakiya a Mali
Wallafawa ranar:
Wani sojan Masar dake aiki da rundunar wanzar da zaman lafiya a Mali ya rasa ran sa yayinda wasu hudu suka samu munanan raunuka bayan da motar dake dauke da su ta taka nakiya.
Lamarin ya wakana ne saman hanyar zuwa yankin Doentza-Boni daf da kan iyaka da Burkina Faso.
Sakatary Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ya bayyana alhinin sa yan lokuta da faruwar harin, tareda jaddada goyan bayan sa zuwa rundunar wanzar da zaman lafiya dake aiki a kasar ta Mali.
Hukumomin Mali na cikin tattaunawa don samar da sabuwar Gwamnati tun bayan da Soumeylou Boubeye Maiga tsohon Firaministan kasar ya ajiye aikin sa sabilin da rashin shawo kan wasu matsalolli da suka jibanci tsaro tun bayan kisan Fulani 160 a tsakiyar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu