Zamfara-Najeriya

Sarakunan Zamfara sun nemi yafiyar sojin saman Najeriya

Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari Mafara
Gwamnan Jahar Zamfara Abdulaziz Yari Mafara wordpress.com

Sarakunan Jihar Zamfara a Najeriya sun nemi gafarar rundunar sojin saman kasar saboda zargin da suka mata na kashe fararen hula da gangan a hare haren saman da ta kai don karkade 'yan bindigar da suka hana zaman lafiya a Jihar.

Talla

Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar, kuma Sarkin Zamfaran Anka Attahiru Ahmed ya gabatar da neman gafarar lokacin da tawagar binciken lamarin da gwamnatin ta kafa ya ziyarci garin Anka a karshen mako.

Basaraken wanda ya bayyana takaici kan matsalar da zargin ya haifar, ya kuma bukaci sojojin su dinga kiyayewa wajen tantance Yan ta’adda da kuma fararen hula lokacin kai harin.

Shugaban tawagar binciken Idi Lubo ya ce sun je Zamfara ne domin tantance abinda ya faru da kuma neman ggafara kan matsalar da aka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI