Afrika

Sojojin Nijar biyar sun mutu a Tahoua

Wani yankin jihar Tahoua a Jamhuriyar Nijar
Wani yankin jihar Tahoua a Jamhuriyar Nijar Pauline Maucort

A Jamhuriyar Nijar, akalla sojan kasar biyar aka tabbatar da mutuwar su yayinda wasu uku suka samu munanan raunuka bayan da motar dake dauke da su ta taka nakiya a dai- dai lokacin da suke kan hanyar su tsakanin Tillia Agendo a yankin Tahoua.

Talla

Ya zuwa yanzu hukumomin kasar basu yi magana a kai ba, sojojin da suka rasa rayukan su na daga cikin rundunar da aka yiwa sunan shara, rundunar da aka samar da ita tun a shekara ta 2016 da kuma keda nauyin tabbatar da tsaro a yankin.

Jamhuriyar Nijar na fama da rashin tsaro a wasu yankunan kasar inda yan jihadi ke ta kokarin wargaza lamarin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.