Ghana na neman 'yan Najeriya 3 kan zargin garkuwa da Jakadan Estonia
Wallafawa ranar:
Rundunar ‘yan sandan Ghana ta yi shelar neman wasu ‘yan Najeriya 3 da ake zargi da sace Jakadan Estonia a kasar Nabil Makram Basbous.
Rundunar ‘yan sandan Ghanan wadda ta yi nasarar ceto Mr Nabil da masu garkuwar suka sace da safiyar Alhamis din da ta gabata, ta ce ‘yan bindigar mutum 3 ‘yan Najeriya ne.
Cikin sanarwar da Kakakin rundunar Efia Tenge ya fitar, ya ce an sace Mr Nabil mai shekaru 61 ne lokacin da ya ke tsaka da tattaki kamar yadda ya saba kowacce safiya a kewayen unguwarsa.
Sanarwar ta ce har zuwa lokacin da ta yi nasarar ceto Jakadan Estoniyan a Ghana, ba ta iya gano wajen da ‘yan bindigar su ke ba.
Rundunar ‘yan sandan dai ba ta bayyana sunan mutanen 3 haka zalika ba ta bayyana hotunansu ba, sai dai ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu