Najeriya-Birtaniya

'Yan bindiga sun hallaka Jami'ar agaji 'yar Birtaniya a Kaduna

Wasu 'yan sandan Najeriya
Wasu 'yan sandan Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da kisan wasu mutane biyu da 'yan bindiga suka yi a karamar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, ciki har da wata ma’aikaciyar agaji 'yar Birtaniya.

Talla

Mai Magana da yawun Yan Sandan Jihar, Yakubu Sabo tare da shugabar kungiyar agajin Mercy Corps, Neal Keny-Guyer sun tabbatar da kashe matar mai suna Faye Mooney.

A cewar rundunar 'yan sandan baya ga kisan mutanen 2 'yan bindigar wadanda ake kyautata masu garkuwa da mutane sun kuma sace mutane 4.

Yakubu Sabo ya ce Yan bindigar sun kutsa kai wajen yawon shakatawar Kajuru ne inda suka harbe Mooney, yayin da suka yi awon gaba da wasu mutane 5, amma daga bisani daya ya kubuce musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI