Bakonmu a Yau

Alhaji Muhammadu Magaji sakataren kungiyar manoma a Najeriya kan gargadin fuskantar kamfar abinci a kasar

Wallafawa ranar:

Bayan gargadin da wani bincike yayi kan barazanar karancin abincin da zai shafi Najeriya a wannan shekara sakamakon rikice rikice a sassan arewacin kasar, yanzu haka kungiyar manoman Najeriya ta bayyana damuwar ta kan rashin daukar matakan da su ka dace domin ganin ba’a fuskanci matsala ba a daminar bana.Dangane da wannan fargaba, mun tattauna da Sakataren tsare tsaren kungiyar manoman Najeriya, Alhaji Muhammadu Magaji kuma ga tsokacin da ya yi mana kan wancan rahoto da kuma halin da ake ciki a Najeriyar.

Wani manomi da ke aikin gyaran gona gabanin faduwar damuna a Najeriya
Wani manomi da ke aikin gyaran gona gabanin faduwar damuna a Najeriya REUTERS/Joe Brock