Najeriya-Dangote-Kano

Dangote ya koka da yawan matasa marasa aikin yi miliyan 4 a Kano

Alhaji Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote REUTERS/Denis Balibouse

Hamshakin Attajirin Najeriya Alhaji Aliko Dangote ya ce muddin shugabanni suka kasa daukar kwararan matakan yaki da talauci da kuma samarwa matasa ayyukan yi, nan da shekaru 5 masu zuwa yawo a titi zai gagare su a fadin Najeriya.

Talla

Aliko Dangote wanda ke bayyana haka ne wajen wani taron tattalin arziki da kuma halin da Kano ke ciki a karshen mako, ya ce ya zama wajibi a duba rayuwar matasa ta hanyar sama musu ayyukan dogara da kai, bunkasa ilimi da kuma wayar da kan al'umma.

Yayin taron wanda ya gudana a Jami'ar Bayero da ke garin na Kano, shugaban sashen nazarin kasuwanci na Jami'ar Farfesa Murtala Sagagi ya ce yanzu haka akwai matasa fiye da miliyan 4 da basu da aikin yi a fadin jihar.

Farfesa Sagagi wanda ya dora alhakin hakan kan matakin rufe kamfanoni fiye da 500 a jihar ta Kano wanda gwamnatocin Najeriya da suka gabata suka yi, ya ce ya zama wajibi a dauka matakan bunkasa bangaren noma don maye gurbin rashin masana'antun.

Hamshakin attajirin na Najeriya Aliko Dangote, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta yi duba kan halin da ake ciki a jihar ta Kano don farfado da kamfanoni tare da bunakasa harkar Noma da galibin al'ummar jihar suka dogara da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.