Afrika ta Kudu

Mutane 33 sun mutu a ambaliyar Afrika ta Kudu

Hukumomin Afirka ta Kudu sun ce, mutane 33 suka mutu sakamakon ambaliya da zabtarewar kasa a birnin Durban, yayinda wasu suka bata, cikin su harda kananan yara.

Mutane da dama sun rasa muhallansu a ambaliyar ruwan Afrika ta Kudu
Mutane da dama sun rasa muhallansu a ambaliyar ruwan Afrika ta Kudu AAP Image/Andrew Rankin/via REUTERS
Talla

Ministar da ke Kula da Yankin Kwazulu-Natal, Nomusa Dube-Ncube ta ce, ruwan sama kamar da bakin kwaryar da aka yi ta shatatawa suka haifar da ambaliya da zabtarewar kasar da suka yi sanadiyar kashe mutanen.

Ministar ta ce, cikin wadanda suka mutu har da wani jariri mai watanni 6 da karamin yaro mai shekaru 10, yayin da wasu yara kanana 10 suka bata, kana wasu mutane 42 suka samu raunuka daban daban.

Wakilin Kamfanin Dillancin labarin Faransa ya ce, da kansa ya ga gawarwakin mutane 9, cikin su har da jariri da aka zakulo a wani gida da ke wajen birnin Durban.

Gwamnatin kasar ta ce, akalla mutane 145 suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI