DR Congo

Mutane sun mutu a hadarin kwale-kwale

Rahotanni daga Janhuriyar Democradiya Congo na cewa an sake samun kifewar wani kwale-kwale, in da nan take mutane 37 suka mutu. Wannan na zuwa ne mako daya bayan da aka samu irin wannan hadari da ya salwantar da rayukan mutane masu yawa.

Kogin Kivu da aka samu hatsarin kwale-kwalen da ya kashe mutane sama da 100 a makon jiya a Jamhuriyar Demokradiyar Congo
Kogin Kivu da aka samu hatsarin kwale-kwalen da ya kashe mutane sama da 100 a makon jiya a Jamhuriyar Demokradiyar Congo MONUSCO/Charles Frisby
Talla

Gawarwaki 16 daga cikin mamatan,  an tsamo su ne a daidai wurin da kwale-kwalen ya kife a kogin gabashin kasar, kamar dai yadda Gwamnan yankin Papy Omeonga Tchopa ya tabbatar.

Kamar yadda yake cewa, musabbabin hadarin abubuwa biyu ne, na farko matukin kwale-kwalen sai da ya yi mankas da barasa, sannan kuma kwale-kwalen ya kwaso mutane da kaya da suka wuce kima.

Mako daya kenan da samun samun irin wannan hadari a kogin Kivu a lokacin da mutane 130 suka salwanta.

Wannan al'amari yasa shugaban kasar Felix Tshekedi ware ranar Juma'a da ta gabata domin zaman makoki a fadin kasar.

Masana sun ce, ana samun mamata ne a irin wannan hatsari saboda yawanci masu shiga kwale-kwalen basa amfani da rigunan kare tsautsayi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI