Faransa

Wasu birane a Faransa na fatan samarwa bakin haure wurin zama

Wasu daga cikin bakin haure a yankin Aubervilliers na kasar Faransa
Wasu daga cikin bakin haure a yankin Aubervilliers na kasar Faransa RFI/Mike Woods

Halin rayuwa da bakin haure suka samu kansu a Faransa ya sa wasu daga cikin magadiyan gari rubuta wasika zuwa hukumomin wannan kasa.Wasu alkaluma na nuni cewa yawan bakin haure da rashin wurin kwancia da ya dace na daga cikin matsallolin da ya hadabi wadanan wakilan jama’a.

Talla

Magadiyan gari 13 na Faransa sun bayyana furicin su ganin halin da bakin haure suka samu kansu, wadanan wakilan jama’a sun bukaci gwamnatin kasar da ta dau matakan da suka dace don samar da karin matsuguni zuwa bakin.

A cikin wasikar da suka aike zuwa hukuma , magadiyan garin sun bayar da shawara na hada karfi don samar da amsa da ta dace tareda dafawa ofishin Ministan cikin gida da mai kula da gine-gine na kasar musaman ganin yawan bakin haure da wasu biranen ke fuskanta yanzu haka.

Kungiyoyi da dama ne yanzu haka suka dau niyar kawo tasu gundumuwa zuwa bakin haure,kama daga France terre D’asile, Emmaus France da wasu kungiyoyin can daban, wanda haka tamkar gundunmuwa take zuwa bukatun magadiyan gari da suka aike da wannan wasika.

Daga cikin magadiyan garin da suka sa hannu a wannan wasika , a kwai magadiyan biranen Lille, Bordeaux,St Denis Aubervilliers, Rennes,Troyes, Metz, Toulouse, Strasbourg, Nantes, Grenoble da Grande Synthe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI