Mozambique

Guguwar Kenneth ta doshi kasar Mozambique

Ambaliyar ruwa a Moçambique.
Ambaliyar ruwa a Moçambique. Reuters

Wata mahaukaciyar guguwa dauke da ruwan sama ta nufi kasar Mozambique a wannan alhamis, wata daya bayan da makamanciyarta ta haddasa mummunar barna da kuma kashe mutane masu tarin yawa a kasar.

Talla

Sabuwar guguwar da masana suna sanya wa suna Kenneth, ta nufi gabar ruwan arewa maso gabashin kasar ne, bayan da ta yi mumman ta’adi a Tsibirran kasar Comoros.

Hukumar kula da hasashen yanayi ta Faransa, ta yi gargadin cewa za ta iya haddasa tumbatsar teku har da mamaye gidaje da gonaki a kasar ta Mozambique.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.