Algeria-Bouteflika

Al'ummar Algeria na ci gaba da zanga-zangar neman sauyi

Al'ummar Ajeriya da ke ci gaba da zanga-zanga a sassan kasar
Al'ummar Ajeriya da ke ci gaba da zanga-zanga a sassan kasar REUTERS/Ramzi Boudina shoul

Dubban al’ummar Algeria yau juma’a sun sake fita kan manyan titunan biranen kasar ciki har da na Algiers babban birnin kasar a ci gaba da zanga-zangar bukatar ganin shugaba Bensalah ya ajje aiki bayan murabus din Abdelaziz Bouteflika da ya shafe shekaru 20 ya na mulkin kasar.

Talla

Zanga-zangar wadda ita ce karo na 10 da ke gudana duk mako a kasar ta Algeria, dubban jama’ar galibi matasa sun fito da kwalaye da ke dauke da rubutun mun gaji da salon mulkin ku, muna bukatar canji.

Shugaba Abdelkader Bensalah, wanda ya maye gurbin Bouteflika dai zai jagoranci kasar ne na tsawon kwanaki 90 gabanin zaben kasar da zai gudana a ranar 4 ga watan Yuni, sai dai ya na fuskantar togiya musamman daga matasan Algeria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI