Afrika

Zaben yan Majalisun Benin na tattare da hatsari

Rikicin siyasar Jamhuriyar Benin
Rikicin siyasar Jamhuriyar Benin rfi hausa

A Jamhuriyar Benin ,yan siyasa bangaren adawa na ci gaba da bayyana damuwa da takaicin su bayan da Shugaban kasar Patrice Talon yayi kunen uwar shegu da bukatar su na dage zaben yan Majalisu na ranar Lahadi 28 ga wannan watan da muke cikin sa .

Talla

A yau juma’a ne ranar kawo karshen yakin zaben na yan Majalisu.

A wasu manyan biranen kasar an samu tawo mu gama da jami’an tsaro ,musaman irin biranen Tchaourou, garin tsohon Shugaban kasar Yayi Boni.

Mutanen garin sun kona motocin yan sanda a wata zanga-zanga da ta gudana a yau juma’a.

Ali Raimi wani dan majalisar wakilai a arewacin kasar ya bayyana damuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI