Afrika

Dokar hana fita daga karfe 3 zuwa karfe 6 a Gombe

Rahotanni daga Gombe dake Najeriya sun ce an kafa dokar hana fita daga karfe 3 na yau asabar zuwa karfe 6 na safiyar gobe, sakamakon wata matsala da aka samu tsakanin wasu matasa da masu daukar gawarwakin mutanen da wani direba ya kashe ranar Easter.

Wasu daga cikin kauyukan arewacin Najeriya masu fama da rashin tsaro
Wasu daga cikin kauyukan arewacin Najeriya masu fama da rashin tsaro RFI/Awwal Janyau
Talla

Rahotanni sun ce matasan sun jefi tawagar masu daukar gawar ne lokacin da suka fito daga asibiti, abinda ya harzuka su suka mayar da martini, wadda ta kaiga samun tashin hankali.

Wannan yasa hukumomi kafar dokar hana fita daga karfe na yammacin yau zuwa karfe 6 na safiyar gobe.

Ya zuwa yanzu dai babu adadi mutanen da suka jikkata sakamakon hargitsin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI