Afrika

Mayakan boko haram sun kwashe tarin makamai a cibiyar binciken Soji a Borno.

Dakarun Najerya dake fada da  yan kungiyar Boko Haram
Dakarun Najerya dake fada da yan kungiyar Boko Haram AFP/ISSOUF SANOGO

Wasu mayakan kungiyar boko haram sun kai hari wata cibiyar binciken soji dake kudancin Jihar Barno inda suka kwashe tarin makamai.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP yace mayakan sun kai harin ne yammacin juma’a kamar yadda majiyoyin soji guda biyu suka tabbatar masa.

Rahotan yace tawagar mayakan cikin motoci sama da 12 dauke da muggan makamai masu sarrafa kan su da kuma motar soji guda 3 da suka kwace suka kai harin.

Majiyar sojin tace, sojin sun yi iya bakin kokarin su amma kuma maharan sun fi su makamai, abinda yasa suka kore su da kwashe makamai.

Wani mazaunin garin Biu dake da nisan kilometa 45 ya sheidawa kamfanin dillancin labaren Faransa cewa ya ganewa idanu sa ta yada da dama daga cikin sojojin Najeriya suka samu shigowa birnin na Biu, yayinda da dama cikin su ,suka samu rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.