Afrika

An sake kashe wani dan Najeriya a Afrika ta kudu

Rikicin kabilanci zuwa baki yan Afrika a Afrika ta Kudu
Rikicin kabilanci zuwa baki yan Afrika a Afrika ta Kudu ibtimes.co.uk

Kungiyar yan Najeriya mazauna Afrika ta kudu tace an sake kashe wani dan kasar Tony Elechukwu, lokacin da wani dan bindiga ya dirka masa harsashi a yankin Witbank Mpumalanga.

Talla

Shugaban yan Najeriya mazauna kasar, Ben Okoli ya tabbatar da aukuwar lamarin a wasikar da ya aikewa ofishin Jakadancin Najeriya a Johannesburg.

Okoli yace wannan shine karo na uku da ake kashe yan najeriya a cikin wannan wata, bayan wadanda aka kashe a ranakun 6 ga wata da 9 ga wata.

Jakadan Najeriya Godwin Adama yayi Allah wadai da kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI