Afrika

Wani hari ya rutsa da malaman makaranta a Burkina Faso

Wani kauye da mahara suka kashe mutane a Burkina Faso
Wani kauye da mahara suka kashe mutane a Burkina Faso Reuters

Wasu yan bindiga da ake zaton mayakan jihadi ne sun kashe mutane shida a wani kauyen Burkina Faso dake yankin Koulpelogo dake tsakiya maso gabacin kasar a jiya juma’a.Daga cikin mutanen da aka hallaka akwai malaman makaranta biyar dake aiki a karamar hukuma ta Comin Yanga.

Talla

Shugaban kasar Marc Roch Christian Kabore ya jaddada cewa babu gudu ba jan da baya a alkawalin da ya yiwa yan kasar na tabbatar da tasro a ilahirin fadin Burkina Faso, kasar dake fama da hare-haren yan jihadi ,kungiyoyin dake kokarin wargaza lamuran tsaro a Burkina Faso da wasu kasashen yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.