Afrika

Babu rikici da ya barke a Kaduna

Yankin Kajuru dake Jihar Kaduna a Najeriya
Yankin Kajuru dake Jihar Kaduna a Najeriya Daily Trust

Rundunar yan Sandan Najeriya ta sanarv da cewa babu wani rikici da ya barke a birnin Kaduna,kamar yadda ake ta yada jita-jita yanzu haka.  

Talla

Mai magana da yawun rundunar dake jihar Kaduna,Yakubu Sabo yace lalle yau an samu  wani da ya saci takalmi a kasuwar Sabo,abinda ya sa mutane suka bi shi da gudu domin kama shi,amma matsalar bata da nasaba da wani sabon rikici.

Sabo yace kwamishinan yan Sandan jihar Ahmed Abdurrahman ya baza jami'an sa cikin Kaduna domin kwantar da hankalin jama'a.

Wasu daga cikin jihohin Najeriya yanzu haka na fama da rashin tsaro,lamarin dake kawo koma baya ga harakokin tattalin arziki da zamantakewa na yau da kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI